Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA, ta bayyana kalaman shugaban kasar Amurika Donald Trump, na zargin yi wa kiristoci kisan kiyashi, a Nijeriya nada alaka da kura-kurai da bayanan bogi da hukumar tattara bayanan sirri ta kasar Amurika ta bashi.
Daraktan hukumar Malam Lanre Issa-Onilu, ne ya bayyana hakan, a wajen taron musanta matsayin Nijeriya kan kalaman Trump, da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.
Lanre Issa-Onilu ya ce zargin da gwamnatin Amurika ta yi babu kamshin gaskiya ko kadan a cikinsa, kuma wannan tsantsar rashin kyautatawa ce ga Nijeriya.
‘’Issa-Onilu ya ce wannan zargi ba gaskiya ba ne, kuma ba adalci ba ne ga Najeriya, domini ta kan ta Amurka ta san cewa babu wani tsari don zaluntar Kiristoci a kasar.
A cewarsa, “Maganar cewa ana kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya ba gaskiya ba ce. Ko Amurka ma ta san haka’’.

