Cibiyar Horas da ‘Yan Jaridu da Samar da Cigaba, CJID, da taƙwararta ta Cibiyar Bincike Aikin Jarida ta Kwakwaf, ta gudanar da wani zagaye na biyu na horas da ‘yan jaridu game da abin da ya shafi sauyin yanayi cikin aikin labarai.
Wannan horaswa na zuwa ne a ƙarƙashin sashen Ƙungiyar Bunƙasa Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO, wacce ita ce kuma ta assasa wannan horaswa.
An dai gudanar da wannan taro ne a Abuja wanda ya samu halartar kafafen yaɗa labarai guda shida daga faɗin ƙasar nan.
A yayin da yake magana a wurin taron, babban daraktan Cibiyar Horas da ‘Yan Jaridu da Samar da Cigaba, Tobi Oluwatola, ya bayyana matsalar sauyin yanayi a matsayin wani ƙalubale da ya shafi duniya gabaɗaya, musamman ma a yankin Afirka saboda dalilai da suka haɗa da talauci da rashin abubuwan more rayuwa da kuma ƙarancin abubuwan amfani na yau da kulum.
Inda ya buƙaci da al’umma su ɗauki matsalar sauyin yanayi a matsayin abu mai muhimmancin gaske.
Waɗanda suka shirya taron dai sun bayyana cewa an zaɓo waɗanda aka horas ne daga kafafen yaɗa labarai da suka haɗa da radiyo da talabijin da kafafen jaridu da kuma kafafen yaɗa labarai na intanet domin isar da saƙon matsalar sauyin yanayi ga al’umma.
The capacity building was part of the project’s mandate in ensuring climate change reporting gains prominence and attention across West Africa.
Mahalarta taron dai sun nuna jin daɗinsu game da samun ƙarin ilimi kan matsalar da sauyin yanayi ke haifarwa tare da nuna muhimmancin horaswar ga kowanne ɗan jarida da ke wayar da kan al’umma a kodayaushe.