• Home  
  • Dakarun Hisba Sun Kama Gandaye A Kano
- Babban Labari - Labarai

Dakarun Hisba Sun Kama Gandaye A Kano

Dakarun Hukumar Hisba masu yaƙi da ɓadala da tabarruji a Jihar Kano, sun kama wasu matasa da ba su yi azumi a ranar farko ta watan Ramadanan bana ba.

Dakarun Hukumar Hisba masu yaƙi da ɓadala da tabarruji a Jihar Kano, sun kama wasu matasa da ba su yi azumi a ranar farko ta watan Ramadanan bana ba.

Mataimakin Kwamanda Janar na Hukumar, Dokta Mujahideen Abubakar ne, ya tabbatar da kama matasan.

Hakazalika, ya tabbatar da cewa jami’an Hisba sun cafke su yayin sintiri da suka yi a sassa daban-daban na Kano.

Har ila yau, hukumar ta kama wasu matasa ku san 60 bisa laifin askin banza, wanda ta ce ya saɓa wa dokokin addini da al’ada.

Bugu da ƙari, an kama wasu direbobin Adaidaita Sahu da ake zargi da cakuɗa maza da mata a cikin abin hawa, abin da hukumar ta ce ba za ta yarda da shi ba.

Hisba ta ce za ta ci gaba da sintiri domin tabbatar da an kiyaye dokokin Shari’a a lokacin watan Ramadan.

 

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000