Dakarun sojojin Nijeriya sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga shida yayin wani aikin sintiri da suka yi a kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa.
A bayanan da Gwamnatin Jihar Kaduna ta samu ya nuna cewa sojojin sun fara aikin sintirin ta hanyar Kaduna-Sabon Birni-Dogon Dawa, har zuwa Maidaro da Ngede Allah, kafin su wuce yankin Saulawa da Kidandan.
A yayin gudanar da wannan aikin ne, sojojin suka yi arangama da ‘yan bindigan a Maidaro, Ngede Allah da kuma Kidandan. Sojojin sun fatattaki ‘yan bindigan har suka yi nasarar kashe ‘yan bindiga shida daga cikinsu.
Sojojin sun yi nasarar kwato bindigogin kirar AK-47 guda biyu, da magazins na AK-47 guda hudu, da alburusai 14, tare da kakin sojoji guda 40. An kuma kama babura guda tara na barayin dajin.
Gwamna Uba Sani ya bayyana jin dadinsa da nasarar da jami’an tsaro suka samu, sannan ya jinjina wa shugaban rundunar sojojin ta daya ta GOC da kwamandan rundunar Operation Whirl Punch, Manjo Janar VO Okoro.
Gwamnan ya yaba wa sojojin bisa kokarin da suke yi, yayin da ya bukace su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na ganin an magance matsalar tsaro a jihar da kasa baki daya.
Sannan an yi kira ga al’umma da su bayar da bayanan sirri na wadanda ake zargin suna da hannu a ayyukan ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga zuwa dakin tattara bayanan tsaro don daukar matakin gaggawa don hukumomin tsaro su dauki mataki, ta layukan waya 09034000060 da 08170189999.
Sannan duk wanda aka samu da raunukan harbin bindiga a jikinsa ko yana neman magani a sirrance a wadannan wurare, to a sanar da hukumomin tsaro kada a ce za a rufa masa asiri.