Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan ya bayyana hukuncin kotun ɗaukaka kara a matsayin koma baya na wucin gadi.
A jiya Alhamis kotun ɗaukaka kara da ke zamanta a Abuja ta ayyana zaɓen gwamnan jihar ta Zamfara a matsayin wanda bai kammala ba. inda ta bayar da umarnin sake gudanar da zaɓe kananan hukumomi uku da suka haɗa da Maradun, Birnin-Magaji da Bukkuyum.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris ya fitar, gwamna Lawal ya ce an zaɓe shi ne saboda ya tsame jihar daga halin kunci da take ciki.
A cewarsa, sakamakon zaɓen gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, ya nuna abin da mutane suka zaɓa musamma na ganin an samu canji mai kyau da kuma ci gaba.
Ya yi kira ga al’ummar Zamfara da su kwantar da hankalinsu, inda ya ce tawagar lauyoyinsa na nazari sosai kan hukuncin domin ɗaukar matakin da ya dace.