598
Dakarun sojojin ‘Operation Hadarin Daji’ a jihar Zamfara sun halaka ƴan bindiga 10 tare da ceto wasu mutum tara da aka yi garkuwa da su.
Hakan na cikin wata sanarwa da rundunar sojin ƙsa ta wallafa a shafinta na Twitter, inda ta bayyana cewa, ƴan bindigan sun taho ne daga jihar Sokoto ta hanyar ƙauyen Gadazaima a jihar Zamfara.