Dalibai huɗu daga Najeriya za su wakilci ƙasar a karon farko a gasar Spelling Bee ta Duniya da za a gudanar a birnin Shanghai na ƙasar China daga ranar 10 zuwa 20 ga Yuli, 2026.
Tawagar ta Najeriya ta ƙunshi Oluwadamilola Adeolu, Abdurrahman Yusuf, Chinedu Okediachi da Maryam Yusuf, waɗanda suka samu tikitin shiga gasar bayan bajintar da suka nuna a gasar Spelling Bee ta Najeriya da kuma ta Afirka.
Masu shirya gasar sun bayyana halartar Najeriya a matsayin wani babban tarihi, suna mai cewa ɗaliban suna ɗauke da fatan al’ummar Najeriya da kuma martabar nahiyar Afirka yayin da za su fafata da fitattun masu iya rubutun kalmomi daga sassa daban-daban na duniya.
Oluwadamilola Adeolu, wadda ta lashe gasar Spelling Bee ta Afirka ta matakin ƙananan yara a Zimbabwe, ta ce tana farin cikin wakiltar Najeriya a matakin duniya, inda ta bayyana fatan lashe kofin tare da dawo da shi gida.
A gasar Spelling Bee ta Afirka da aka gudanar a Harare, Najeriya ta zo ta biyu gaba ɗaya, yayin da Adeolu ta zama zakara a ajin ƙananan yara, sannan Abdurrahman Yusuf ya zo na uku. Masu shirya gasar sun ce wannan nasara ta nuna ci gaban da Najeriya ke samu a gasa ta ilimi a matakin ƙasa da ƙasa.
