Jam’iyyar ADC a Najeriya da kuma ɗantakararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar sun yanke shawarar ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙolin Najeriya kan hukuncin shugabancin jam’iyyar.
A ranar Litinin ne kotun ɗaukaka ƙara da umarci hukumar zaɓen ƙasar INEC ta daina amincewa da tsagin David Mark a matsayin shugabannin jam’iyyar.
Cikin wasu mabambantan sanarwa da ADC da Atiku suka fitar, sun ce za su ƙalubalanci hukuncin a Kotun Ƙolin ƙasar.
Kotun ɗauka ƙarar ta tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya wadda ta hana INEC amincewa da tarukan jam’iyyar na ƙasa da jihohi, wanda a nan ne aka zaɓi shugabannin ɓangaren David Mark.
Atiku da ADC sun buƙaci lauyoyinsu su tattara duka bayanan da suke buƙata domin ɗaukaka ƙarar.
ADC ta jima tana fama da rikicin shugabanci, wani abu da masana ke gani a matsayin barazana ga shirye-shiryen jam’iyyar don tunkarar zaɓen 2027.

