Matatar Dangote ta sanar da dakatar da sayar da mai ga masu sari da kuɗin Najeriya naira.
A ranar 1 ga watan Oktoban 2024 ne dai Dangote ya fara sayar da mai na naira ga kwastomominsa a Najeriya, bayan cimma wata yarjejeniya da gwamnatin ƙasar, kan wadata ƙasar da man fetur.
A lokacin an cimma yarjejeniyar cewa gwamnatin Najeriya za ta riƙa sayar masa da ɗanyen mai da naira yayin da shi ma zai riƙa sayar da wanda ya tace da naira.
Kawo yanzu dai babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da Dangoten ya bayar dangane da wannan mataki, to amma wasu jaridun ƙasar na ambato wasu majiyoyi a matatar na cewa a yanzu gwamnati na sayar da matatar ɗanyen mai ne da dala, kuma ba ta sayar mata wanda zai wadace ta.
