Kokawar gargajiya dai a kasar Nijar ta samo asali tun gadin-gadin ko muce tun kaka da kakanni.
Haka zalika masu fara ta tun suna kananu akan kira ta da suna tafastaka a sassa daban-dsban na kasar ta Nijar wadda take a yammacin Afrika.
A dukkanin karshen ko wacce shekara idan za a gudanar da bikin wannan gasa, dukkanin jihoshin Nijar su kan hadu domin fafatawa da juna.
A karshen wannan shekarar dai ta 2024 da aka kammala kokawar a jihar Dosso jihar Niamey ta yi sabon ango inda Abba Ibrahim ya samu sabon kambun na gasar ta kokawa bayan ya lallasa shahararre kuma gagarabadau a duniyar kokawa wato Isaaka Isaaka na jihar Dosso a gaban magabata.
Wani babban abin takaici ga al’ummar jihar ta Dosso a jihar aka gudanar da kokawar inda su ka so suyi gagarumin bikin lashe takobi ganin a gidan su ake gudanar da wannan kokawa.
Ganin yadda Isaaka Isaaka ya shahara a gasar kokawa kuma shine danwasan da yafi kowa yawan lashe gasar idan akayi daidaikuwa, kashi 90 cikin 100 ake bashi nasarar shine zai lashe gasar, amma kuma Abba Ibrahim ya yimasa fancale a wasan karshe a gaban iyaye da kakanni.
A wannan safiya ta Talata daya daga cikin ma’aikatan gidan talabijin da rediyo na Muhasa wadda take a jihar Kano a Najeriya wato Suraj Na’iya Kududdufawa ya tattauna da Abba Ibrahim ta wayar tarho inda ya yimasa tambaya game da nasarar da ya samu.
“Farko ina yiwa Allah godiya da na zamo zakara kuma naso naji tsoro a lokacin da Isaaka Isaaka ya so yimin wata raruma amma naga nima namiji ne to bai cafkeni a dai-dai ba nikuma na kwakwashe shi na turashi ya kife da gefen kafadarsa ta dama nikuma na doshi ‘yan kallo ina cika baki domin na kayar da wanda ya gagara a wasan kokawa a kasar Nijar”.
Saidai manyan dalilan da su ka sanya aka lallasa Isaaka Isaaka sune, mafi yawa jihar da ta da karbi bakuncin gasar bata iya lashewa domin hakan ta faru da dama sai dai dan jihar yayi dan galadima kamar yadda ta faru a jihar ta Dosso.
Dalili na biyu kuwa shine ko wacce jiha a kasar Nijar tana jin haushin Isaaka Isaaka yadda ya addabi mutane a wasan kokawar gargajiya kuma yafi kowa lashe takobi.
Jihar Maradi ce dai tafi ko wacce jiha yawan lashe takobi sannan mai biyemata jihar Damagaran sai kuma jihar Dosso da sauran su.