Ministan tsaro na Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya ajiye aikinsa daga yau Litinin, 1 ga Disamba, 2025, bisa dalilan lafiya.
Wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta fitar ta ce Badaru ya sanar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu murabus ɗinsa a cikin wasiƙar da ya aika masa, inda ya ce ya yi hakan ne domin samun damar kula da lafiyarsa.
Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin, tare da gode wa Badaru bisa gudunmawar da ya bayar tun bayan nadinsa a shekarar 2023.
- Gwamnonin Arewa za su kafa gidauniyar yaƙi da matsalar tsaro a yankin
- Ƙananan Hukomomin Kano 44 sun kare kasafin kuɗin 2026
Fadar shugaban ƙasa ta ce ana sa ran shugaban ƙasar zai tura sunan wanda zai maye gurbin kujerar ga majalisar dattawa a cikin mako mai zuwa.
Badaru Abubakar, mai shekaru 63, tsohon gwamnan jihar Jigawa ne da ya yi wa’adanni biyu daga 2015 zuwa 2023, kafin nadinsa a matsayin ministan tsaro.
Murabus ɗin nasa ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkokin tsaro.
