Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin ceto dukkanin mutanen da aka yi garkuwa da su a garuruwan Sandu da Yan Chibi dake kananan hukumomin Tsanyawa da Sahanono da Yan bindiga suka yi garkuwa da su a kwanakin bayan nan.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da tabbacin Hakan ne yayin da ya kai ziyarar gani da idanu garuruwan da abun ya shafa a ranar Talata, inda ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da hada karfi da karfe da dukkanin hukumomin tsaron jihar domin magance matsalar tsaro.
Gwamnan ya kara da cewa, matsalar tsaron da ta fara kunno kai a jihar Kano wani sabon al’amari ne da al’ummar jihar basu san shi ba kuma gwamnatin za ta cigaba da yin duk mai yiyuwa domin ganin ta magance wannan matsalar.
Haka zalika gwamna Abba Kabir Yusuf ya Kuma bayar da tabbacin inganta walwalar hukumomin tsaro yadda ya kamata domin ganin an kawo karshen matsalar tsaro a fadin jihar.
