Zaɓaɓɓen ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Rogo, Jibrin Ismail Falgore, ya zama shugaban majalisar dokoki ta jihar Kano karo ta 10.
Falgore ya yi nasarar zama shugaban majalisar ne ba hamayya bayan da dan majalisar Dala na jam’iyyar NNPP ne ya ayyana falgore a matsayin wanda yake ganin dacewarsa wajen shugabantar majalisar.
Nan da nan ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Takai, Musa Ali Kachako, daga jam’iyyar APC ya mara masa baya.
Sannan kuma dan majalisa mai wakiltar Rimingado da Tofa Muhammad Bello Butubutu daga jam’iyyar NNPP ya yi nasarar zama mataimakin majalisar dokokin ta jihar Kano.
Shi ma ya haye wannan kujera ne batare da hamayya ba bayan Zubairu Hamza Masu mai wakiltar Sumaila daga jam’iyyar NNPP ya ayyana shi a matsayin wanda ya dace da zama mataimakin Falgore.
Jam’iyyar NNPP ce dai take da rinjayen da yawan ‘yan majalisu 26, sai kuma APC ‘yan majalisu 14.