Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ya ji daɗi kan yadda Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu yake nemansa don kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa.
Tinubu ya yi masa tayin muƙami a gwamnatin, sai dai Kwankwaso ya ce har yanzu ba su kai ga cimma matsaya ba.
Sanata Kwankwaso ya bayyana haka ne lokacin da yake bayyana wa manema labarai abin da ya wakana tsakaninsa da shugaba Tinubu.
Tattaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da dambarwa ke ƙara kamari tsakanin ɓangaren sabuwar gwamnatin Kano da kuma gwamnatin APC da ta shuɗe.