Hukumar zaɓe mai zaman kanta a jihar Zamfara ta bayyana Dauda Lawal Dare a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.
Dauda Lawal dai ya samu ƙuri’u 377,726 – inda ya yi nasara a kan gwamna mai ci Bello Muhammad Matawalle wanda ya samu ƙuri’u 311,976.
An dai kwashe tsawon lokaci ana tattara sakamakon zaɓen biyo bayan jinkiri da aka samu.
Rahotanni da suka fito daga jihar sun ce an sace jami’an tattara sakamakon zaɓe a kan hanyarsu ta zuwa Gusau, babban birnin jihar, daga ƙaramar hukumar Maradun.
Sai dai rahotonni sun nuna cewa an saki jami’an daga baya.