Home » Daukar mataki kan Nijar zai kara rura wutar rikici ne a yankin Sahel ~ Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo

Daukar mataki kan Nijar zai kara rura wutar rikici ne a yankin Sahel ~ Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo

by Anas Dansalma
0 comment
Daukar mataki kan Nijar zai kara rura wutar rikici ne a yankin Sahel ~ Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo

Fitaccen Malamin Addinin Islama, Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo, ya ja hankalin Shugaban Bola Ahmed dangane da daukar matakin da zai kara rura wutar rikici a yankin Sahel.

Gargadin fitaccen malamin na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya shaida wa Majalisar Dokoki matsayar da kungiyar ECOWAS ta cimma kan daukar matakin soji a kan Nijar da kuma sauran takunkuman da aka dauka na ladabtar da sojojin da suka yi juyin mulki.

A lokacin da yake gabatar da karatu, Sheikh Rijiyar Lemo ya ce akwai bukatar ECOWAS karkashin jagorancin Shugaba Tinubu ta sake nazari domin kuwa alakar da ke tsakanin Nijar da Najeriya ta zarce ta makwabtaka ta kai matsayin ’yan uwantaka.

A cewarsa, muddin sojoji suka kai mamaya Jamhuriyyar Nijar, to kuwa babu shakka hakan zai kara rura wuta a kan dimbin kalubalen zamantakewa da tattalin arziki a yankin Sahel, inda yake shawartar ECOWAS ta da ta sake tunani.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?