Mai ba wa Gwamnan Kano Shawara kan harkokin matasa da wasanni, ya rushe shugabancin kungiyar Matasa ta kasa reshen Kano.
Wannan dai na zuwa ne bayan da wa’adin shugabancin kungiyar ya kare, kuma tuni aka sanar da rushe su baki daya.
Cikin wata sanarwar da ofishin mai bawa Gwmanan na Kano Shawara kan harkokin matasa da wasanni Amb Yusuf Imam Ogan Boye ya fitar a wannan Juma’ar ta ce, tuni aka maye gurbinsu da wasu wanda za su jagoranci shugabancin kungiyar.
Sanarwar ta kara da cewa Muhammad El-Gambo zai zama sabon shugaba, sai Jamilu D. Attahir a matsayin Sakatare.
Sauran sun hada Ahmad Yusuf Godiya da Abubakar Ali Ado da Bala Musa Kwankwaso, Yusuf Imam T/Wada da Garba Ayuba Falo zasu kasance sabbin Mambobi a kungiyar matasa ta kasa reshen Jihar Kano.