• Home  
  • Dele Momodu Ya Fice Daga PDP
- Babban Labari - Labarai

Dele Momodu Ya Fice Daga PDP

Fitaccen ɗan siyasa kuma tsohon gogaggen ɗanjaridar nan na Najeriya, Dele Momodu ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa sabuwar haɗakar ADC ta an hamayya. Domodu – wanda ya taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasar – ya ce ya ɗauki matakin ne saboda yadda wasu da ya kira ”masu yaƙi da dimokraɗiyya” suka hana jam’iyyar numfashi. […]

Fitaccen ɗan siyasa kuma tsohon gogaggen ɗanjaridar nan na Najeriya, Dele Momodu ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa sabuwar haɗakar ADC ta an hamayya.

Domodu – wanda ya taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasar – ya ce ya ɗauki matakin ne saboda yadda wasu da ya kira ”masu yaƙi da dimokraɗiyya” suka hana jam’iyyar numfashi.

Cikin wasiƙar ficewar tasa da ya aike wa shugaban jam’iyyar na mazaɓarsa ta Ihievbe a ƙaramar hukumar Owan ta Gabas, ranar Alhamis 17 ga watan Yuli, fitaccen ɗansiyasar ya ce dole ce ta sa ya ɗauki matakin domin maido da martabar dimokraɗiyya.

“Dalilina a bayyane yake, wasu masu yaƙi da dimokraɗiyya sun maƙure jam’iyyar daga ciki da wajen jam’iyyar”, kamar yadda wani sashe na wasiƙar ya nuna.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000