• Home  
  • Jami’ar Yan Sandan Nijeriya Dake Wudil Ta Fara Binciken Masu Yunkurin Damfarar Jama’a Ta Yanar Gizo
- Babban Labari - Labarai

Jami’ar Yan Sandan Nijeriya Dake Wudil Ta Fara Binciken Masu Yunkurin Damfarar Jama’a Ta Yanar Gizo

Rahotanni na cewa jami’ar yan sandan Nijeriya dake garin Wudil, a jihar Kano ta fara gudanar bincike kan wasu batagarin mutane da ake zargi da aikewa da mutane sakonnin su bayar da kudi ta yanar gizo-gizo don basu gurbin karatu a jami’ar. Kakakin jami’ar yan sandan Nijeriya dake Wudil, DSP Umar Musa Isah, ne ya […]

Rahotanni na cewa jami’ar yan sandan Nijeriya dake garin Wudil, a jihar Kano ta fara gudanar bincike kan wasu batagarin mutane da ake zargi da aikewa da mutane sakonnin su bayar da kudi ta yanar gizo-gizo don basu gurbin karatu a jami’ar.

Kakakin jami’ar yan sandan Nijeriya dake Wudil, DSP Umar Musa Isah, ne ya tabbatar da fara gudanar da bincike bayan samun korafe-korafe daga wajen jama’a.

DSP Umar ya ce yanzu haka kwamandan jami’ar yan sandan, AIG Patrick Adedeji Atayero, ya bada umarnin yin bincike don gano su waye masu yunkurin yin damfarar.

Ya kara da cewa yakamata mutane su sani cewa babu wani ma’aikaci, a jami’ar da zai kira mutum ya nemi ya tura kudi kafin ba su gurbin karatu, inda ya ce form din ma ba a jami’ar ake siyar dashi ba don haka duk wanda ya tura kudi to an damfare shi.

Yaja hankalin jama’a musamman wadanda suke nemen gurbin karatu a jami’ar da su sani cewa bisa cancanta ake dauka ba ta hanyar damfara ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000