Hukumar tsaro ta farar kaya DSS, ta shaidawa babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja hikimar cigaba da tsare Godwin Emefiele.
Inda ta ce, tsohon Gwamnan na babban bankin kasa na CBN zai tsere daga Najeriya ne muddin aka ba shi beli.
Jami’an tsaro sun bayyana Emefiele a matsayin barazana ta fuskar hawa jirgin sama ya bar Najeriya yayin da ake kokarin cigaba da bincike a kansa.