Rundunar tsaro Ta farin kaya wato DSS ta ce tana sane da shirye-shiryen da wasu bata gari ke yi na kawo tarnaki yayin bikin rantar da shugaban kasa da gwamnoni a ranar 29 ga watan Mayu a fadin kasar .
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Peter Afunanya, ya saki a yammacin jiya Alhamis.
Afunanya ya ce manufar ita ce kawo cikas ga kokarin hukumomin tsaro wajen tabbatar da gudanar da bikin cikin zaman lafiya da haifar da tsoro da fargaba tsakanin al’umma,
Kakakin rundunar ya kara da cewar ana gargadin wadanda ba a ba izini ba da su nisanci wuraren da aka kebe da wasu wurare na musamman a wajen taron.