• Home  
  • DSS ta gurfanar da mutum biyar kan zargin sace ƴan NYSC a Imo
- Labarai

DSS ta gurfanar da mutum biyar kan zargin sace ƴan NYSC a Imo

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Najeriya (DSS) ta gurfanar da wasu mutum biyar da ake zargi da hannu a sace wasu masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) 20 da wani farar hula a jihar Imo. An gurfanar da waɗanda ake zargin a babbar kotun jihar Imo da ke Owerri bayan kama su a wasu […]

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Najeriya (DSS) ta gurfanar da wasu mutum biyar da ake zargi da hannu a sace wasu masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) 20 da wani farar hula a jihar Imo.

An gurfanar da waɗanda ake zargin a babbar kotun jihar Imo da ke Owerri bayan kama su a wasu samame da jami’an tsaro suka gudanar bisa bayanan sirri a jihohin Rivers da Abia.

An sace matasan masu yi wa ƙasa hidimar da farar hular ne a ranar 1 ga Oktoban 2026 a kusa da Umunoha da ke ƙaramar hukumar Mbaitoli, yayin da suke kan hanyarsu daga Ibadan zuwa sansanonin horaswa na NYSC a jihohin Abia da Akwa Ibom.

Lamarin da ya sa jami’an tsaro suka kaddamar da wani samame, inda aka ceto mutanen 21 a ranar 7 ga Oktoba daga dajin Amakohia-Ubi da ke ƙaramar hukumar Owerri ta Yamma.

Daga baya DSS ta ce ta kama mutum biyar tsakanin 10 da 14 ga Oktoba a Port Harcourt da Aba, waɗanda yanzu haka suke fuskantar shari’a.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai