• Home  
  • Ambaliya ta kashe mutum 2, ta raba wasu 4,000 da gidajensu a Nasarawa
- Babban Labari

Ambaliya ta kashe mutum 2, ta raba wasu 4,000 da gidajensu a Nasarawa

Ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar mutum biyu tare da raba wasu sama da 4,000 da muhallansu a Jihar Nasarawa, bayan da ta mamaye ƙauyuka da dama tare da lalata gidaje da gonaki. Mazauna yankunan da abin ya shafa, musamman a Ƙaramar Hukumar Doma, sun ce ruwan ya fara mamaye gidaje da gonaki ne kimanin […]

Ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar mutum biyu tare da raba wasu sama da 4,000 da muhallansu a Jihar Nasarawa, bayan da ta mamaye ƙauyuka da dama tare da lalata gidaje da gonaki.

Mazauna yankunan da abin ya shafa, musamman a Ƙaramar Hukumar Doma, sun ce ruwan ya fara mamaye gidaje da gonaki ne kimanin makonni biyu da suka gabata, bayan ƙarin ruwa a Kogin Benuwai.

Wasu iyalai sun rasa amfanin gonakin da suka dogara da su wajen ciyar da iyalansu da biyan kuɗin makarantar ’ya’yansu.

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Nasarawa (NASEMA) ta bayyana cewa sama da mutane 4,000 ne ambaliyar ta raba da muhallansu, yayin da gwamnatin jihar ta tabbatar da mutuwar mutum biyu.

Ambaliyar ta kuma katse hanyar mota daga Doma zuwa yankunan da abin ya shafa, lamarin da ya tilasta tawagar tantance barnar yin amfani da jirgin ruwa domin isa gare su.

Gwamnatin jihar ta ce tana shirin kai kayan agaji ga waɗanda abin ya shafa, ciki har da abinci, katifu, barguna da kayan gini.

Ta kuma gargaɗi mazauna yankunan da ke ƙasa da matakin ruwa da su koma wurare masu tudu, tare da guje wa komawa gidajensu har sai ruwan ya janye gaba ɗaya.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai