Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da hannu a sace Alhaji Kabiru Aliyu a ƙauyen Falgore da ke ƙaramar hukumar Doguwa, tare da ƙwato bindigar AK-47 da alburusai 18 a dajin Falgore.
Sanarwar da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ta ce an kama wanda ake zargin mai suna Ibrahim Rabiu, ɗan ƙauyen Yardoka a ƙaramar hukumar Kubau ta Jihar Kaduna, ranar 18 ga Oktoba, 2026.
An ce kamen ya biyo bayan wani samame da jami’an ’yan sanda na Doguwa suka gudanar tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai domin gano waɗanda ake zargi da aikata laifin da kuma ƙwato makaman da suka yi amfani da su.
Rundunar ta ce wanda aka ceto ya gane wanda ake zargin a matsayin mutumin da ke tsaron sa da dare a lokacin da yake tsare, yake kai masa abinci tare da dukansa.
A halin yanzu, an miƙa wanda ake zargin ga sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin zurfafa bincike da kuma kamo sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.
Kwamishinan yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da ƙoƙarin yan sa-kai wato ( ’Yan Bula) wajen taimaka wa rundunar wajen tabbatar da tsaro a dajin Falgore da sauran al’ummomin da ke yankin.
Wannan na zuwa ne bayan sanarwar rundunar ta ranar 17 ga Oktoba, wadda ta ce an kashe wasu da ake zargin ’yan bindiga ne guda biyu, tare da ceto Alhaji Kabiru Aliyu da kuma ƙwato kuɗin fansa naira miliyan 10.
