Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Najeriya (DSS) ta gurfanar da wasu mutum biyar da ake zargi da hannu a sace wasu masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) 20 da wani farar hula a jihar Imo.
An gurfanar da waɗanda ake zargin a babbar kotun jihar Imo da ke Owerri bayan kama su a wasu samame da jami’an tsaro suka gudanar bisa bayanan sirri a jihohin Rivers da Abia.
An sace matasan masu yi wa ƙasa hidimar da farar hular ne a ranar 1 ga Oktoban 2026 a kusa da Umunoha da ke ƙaramar hukumar Mbaitoli, yayin da suke kan hanyarsu daga Ibadan zuwa sansanonin horaswa na NYSC a jihohin Abia da Akwa Ibom.
Lamarin da ya sa jami’an tsaro suka kaddamar da wani samame, inda aka ceto mutanen 21 a ranar 7 ga Oktoba daga dajin Amakohia-Ubi da ke ƙaramar hukumar Owerri ta Yamma.
Daga baya DSS ta ce ta kama mutum biyar tsakanin 10 da 14 ga Oktoba a Port Harcourt da Aba, waɗanda yanzu haka suke fuskantar shari’a.

