• Home  
  • Yadda Aka Karrama Janar Murtala Muhammed A Abuja
- Babban Labari - Labarai

Yadda Aka Karrama Janar Murtala Muhammed A Abuja

Manyan mutane sun hallara a Abuja, a ranar Juma’a, domin tunawa da cika shekaru 50 da kisan tsohon Shugaban ƙasa, Janar Murtala Muhammed. An kashe marigayi Janar ne tare da wasu muƙarrabansa, a wani yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba a Legas, ranar 13 ga Fabrairu, 1976. Jami’an rundunar sojin Najeriya sun yi […]

Manyan mutane sun hallara a Abuja, a ranar Juma’a, domin tunawa da cika shekaru 50 da kisan tsohon Shugaban ƙasa, Janar Murtala Muhammed.

An kashe marigayi Janar ne tare da wasu muƙarrabansa, a wani yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba a Legas, ranar 13 ga Fabrairu, 1976.

Jami’an rundunar sojin Najeriya sun yi bikin karrama shi tare da wasu manyan baƙi.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Farfesa Ibrahim Gambari, fitaccen jami’in diflomasiyya kuma tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa lokacin mulkin marigayi Muhammadu Buhari.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai