DSS Ta Mayar Da Nnamdi Kanu Gidan Yarin Sokoto

Hukumar DSS ta mayar da Shugaban ’Yan Awaren Biyafara (IPOB), zuwa gidan gyaran hali a Jihar Sakkwato.

Wannan mataki ya biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke masa na ɗaurin rai da rai kan laifukan ta’addanci.

A ranar Alhamis ne, Alƙalin Kotun Tarayya da ke Abuja, James Omotosho, ya ce DSS za su kai Kanu kowace cibiyar gyaran hali da ke Najeriya.

Lauyan Kanu, Aloy Ejimakor, ya tabbatar da mayar da shi Sakkwato aranar Juma’a.

Ya ce: “DSS ta ɗauke Mazi Nnamdi Kanu daga gidan yari na Abuja zuwa  Sakkwato, sun nesanta shi da lauyoyinsa, iyalinsa, da masoyansa.”

An yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai kan laifuka bakwai da suka shafi ta’addanci.

Kotun ta tabbatar da cewa Kanu ya yi amfani da ta’addanci wajen raba yankunan Kudu-Maso Gabas da Kudu Maso Kudu, da wasu sassan Binuwai da Kogi daga ma Najeriya baki ɗaya.

Hukumomin shari’a sun kuma buƙaci a rufe dukkanin shafukan Kanu, tare da tabbatar da cewa yana cikin tsaro domin ba shi kariya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *