• Home  
  • Matawalle Ya Isa Birnin Kebbi Bisa Umurnin Tinubu
- Babban Labari - Labarai

Matawalle Ya Isa Birnin Kebbi Bisa Umurnin Tinubu

Ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Mohammed Bello Matawalle ya isa tashar jirgin sama ta Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi, domin taimaka wa da sa ido kan yunƙurin ceton ɗaliban da aka sace a jihar ta Kebbi. A ranar alhamis ne Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya umarce shi ya koma jihar – da ke arewa […]

Ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Mohammed Bello Matawalle ya isa tashar jirgin sama ta Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi, domin taimaka wa da sa ido kan yunƙurin ceton ɗaliban da aka sace a jihar ta Kebbi.

A ranar alhamis ne Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya umarce shi ya koma jihar – da ke arewa maso yammacin Najeriya – har sai an dawo da ɗaliban gida.

A farkon wannan mako ne wasu ƴanbindiga riƙe da muggan makamai suka shiga makarantar Sakandiren ƴanmata da ke garin Maga a yankin ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a jihar tare da sace ɗalibai 25.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai