Dubban ’Yan Gudun Hijira Sun Koma Gidajensu A Zamfara — ’Yan Sanda

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Zamfara ta taimaka wa dubban ’yan gudun hijira  komawa garinsu na asali, wato ƙauyen Fegin Kanawa da ke Ƙaramar Hukumar Gusau.

Sun koma ne bayan kusan shekara guda suna gudun hijira sakamakon hare-haren ’yan bindiga da suka addabi yankin.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Yazid Abubakar ya fitar, ya bayyana cewa wannan mataki ya yi daidai da ƙuduri da kuma dabarun Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar, CP Ahmad Muhammad Bello na dawo da doka,  ƙarfafa gwiwar al’umma, da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a faɗin jihar.

CP Ahmad Muhammad ya tabbatar wa ’yan gudun hijirar da suka koma cewa, an samar da gamsassun matakan tsaro domin su ci gaba da ayyukan noma da sauran harkokin neman halak ba tare da fargabar hare-hare, garkuwa da mutane ko tursasawa daga ɓata-gari ba.

Duk da haka, CP Ahmad Muhammad Bello ya sake jaddada ƙudurin rundunar na kau da ayyukan ta’addancin ’yan bindiga da dukkan nau’ukan miyagun laifuka na tashin hankali a jihar, inda ya jaddada cewa ba za a bar wani wuri na ɓoyewar masu laifi ba a Jihar Zamfara.

An dai kwashe sama da shekara guda ana barin ƙauyen Fegin Kanawa ba kowa, bayan da mazauna garin suka tsere sakamakon hare-haren ’yan fashi.

Post masu alaƙa

Tinubu ya yaba wa gwamnonin APC kan zaɓen fitar da gwani

Ɗan Ganduje Ya Sayi Fom Ɗin Takarar Majalisar Tarayya A NDC