Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama dan bindiga da sanye da kayan sojoji.

Rundunar yan yandan jihar Kano ta samu gagarumar nasara a yaƙi da masu aikata manyan laifuka, Inda  kama wani mutum da ake zargin yana kai wa ‘yan bindiga kayan kayayyaki  a ƙaramar hukumar Bichi.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar, 12 ga Yulin 2026, bayan da wani mutum ya sanarwa da ‘yan sanda cewa an ga wani mutum sanye da kayan da ake zargin na sojoji a ƙauyen Rimaye da ke ƙaramar hukumar Bichi.

Ya ce jami’an ‘yan sandan Bichin tare da haɗin gwiwar al’ummar Rimawa, sun yi gaggawar zuwa wurin, inda suka kama wanda ake zargin mai suna Mohammed Isah Haruna, mai shekaru 28, mazaunin unguwar Dan Dinshe Yamma a ƙaramar hukumar Dala.

Binciken da aka gudanar ya kai ga ƙwato kwanson bindigar AK-47 cike da harsasai 30 da karin wasu harsasai 79 da kayan sojoji da  hulunan sojoji guda uku, ID Card din sojoji na bogi da  takalman sojoji da sauran kayayyaki.

A cewar rundunar, yayin tambayoyi wanda ake zargin ya amsa cewa ya je yankin ne domin kai kayayyaki ga ‘yan bindigar da ke cikin daji.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa al’ummar Rimawa bisa nuna kishin ƙasa da kuma gaggawar isar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro.

Ya ce haɗin kan al’umma da jami’an tsaro shi ne ginshiƙin samun zaman lafiya da nasarar yaƙi da miyagun laifuka, tare da yin kira ga al’ummar jihar Kano su ci gaba da bai wa ‘yan sanda sahihan bayanan da za su taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyinsu.

Rundunar ta ce wanda ake zargin yana tsare kuma ana ci gaba da zurfafa bincike domin ganowa tare da kamo sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin kafin gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.

Post masu alaƙa

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya

Majalisar Wakilai ta janye kudirinta kan ‘yan sandan jihohi tare da yin nazari kan buƙatar Tinubu

ADC da Atiku sun ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Koli