Daga: Safiyanu Haruna Kiyama
Ƙungiyar bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ta ce ta yi shirin da zai saukaka tattaunawa da ƙasashen Burkina Faso da Mali da kuma Nijar, waɗanda ke karkashin jagorancin mulkin soji da suka fice daga ƙungiyar a hukumance ranar 29 ga wannan watan.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a safiyar yau Laraba, Hukumar ta ce tana shirin kaucewa ruɗani da hargitsi a cikin rayuwa da kasuwancin mutanen da ke kasashen ECOWAS da kuma waɗanda ke yankin Sahel, a lokacin da ɓangarorin biyu ke raba gari.
A cewar ECOWAS, “Ficewar Burkina Faso da Mali da Jamhuriyar Nijar daga ECOWAS ya fara aiki daga yau 29 ga watan Janairu 2025, Duk da haka, a cikin mutunta zamantakewa da inganta haɗin kai a yankin da kuma muradun jama’a, ECOWAS ta bukaci dukkan hukumomin da abin ya shafa a ciki da wajen ƙasashen ƙungiyar ta ECOWAS da su ƙyale ƴan ƙasashen uku su ci-gaba da cin gajiyar ƴancin shige da fice ba tare da buƙatar biza ba, da damar zama a cikin ƙasashe kamar yadda ka’idojin ECOWAS suka tanada na tsawon wani lokaci”.
Sanarwar ta ƙara da cewa ECOWAS za ta ci-gaba da amincewa da takardun tafiye-tafiye da katin shaida mai ɗauke da tambarin kungiyar ECOWAS da ke hannun ƴan ƙasashen AES, sannan a ci-gaba da mutunta kayayyaki da ayyukan da ke fitowa daga ƙasashen uku bisa tsarin kasuwancin manufofin saka hannun jari na ECOWAS.
Hukumar ta yi nuni da cewa, za’a gudanar da wadannan tsare-tsaren har sai majalisar shugabannin ƙasashen ECOWAS ta kammala tantance hanyoyin da za a ci-gaba da hulɗa da ƙasashen uku nan gaba.
Kungiyar ECOWAS ta ce ƙasashen na Sahel na da wa’adin watanni shida da zai ƙare a watan Yuli, domin sake duba matsayinsu, ko da za su sauya ra’ayi kan ficewa daga ƙungiyar.