Jam’iyyar Labour a jihar Edo da ke kudancin ƙasar nan ta bayyana cewa duk ɗan takarar da ba zai iya biyan kuɗin sayen form ɗin nuna sha’awar tsayawa takara da fom tsayawa takara na gwamnan jiha a jam’iyyarsu ba, to sam bai cancanci tsayawa takarar ba.
Wannan na zuwa ne gabanin zaɓen cikin gida da kuma zaɓen gwamnan jihar da ake sa ran yi a watanni masu zuwa.
Shuagaban jam’iyyar reshen jihar Edo, Ogbalol Kelly, ya bayyana hakan a jiya Laraba a yayin da yake yin ƙarin haske kan kuɗin fom na Naira miliyan 30 da jam’iyyar ta gindaya ga duk mai son tsayawa takara a jam’iyyar.
Ya ce miliyan 30 da jam’iyyar ta sa ka na fom ɗin tsayawa takarar gwamna shi ne mafi ƙarancin kuɗi, idan aka kwatanta da na sauran jam’iyyu.
Ya ce ana ci gaba da samun ƙaruwar kuɗin da ake kashewa a yayin neman wata kujera a Najeriya saboda sauyin yanayi na abubuwa da dama a ƙasar nan kamar yadda babban zaɓen 2023 ya nuna.
Ya ƙara da cewa baya ga cancanta, wajibi mai sha’awar tsayawa takara ya zama yana da ƙarfin da zai iya ɗaukar nauyin camfen da sauran tsarabe-tsaraben harkokin zaɓe.
Kuma ya ce ta hanyar sayar da fom ne kaɗai jam’iyyu ke samun kuɗin gudanar da ayyukansu, inda ya tabbatar da cewa tuni mutane biyu mace ɗaya da namiji suka sayi fom ɗin tare da roƙon sauran masu sha’awa da su gaggauta siyan nasu kafin ƙarewar wa’adin siyarwa.