Ƙasar Mali a maimakon ƙasashen Burkina Faso da Nijar, ta rubuta wa ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma, wato ECOWAS, takardar sanarwa na ficewa daga ƙungiyar nan take.
ƙasashen sun zargi ƙungiyar da sauka daga manufofin da suka assasa kafa ƙungiyar waɗanda ke ƙunshe da aƙidar bunƙasa yankin Afirka.
Sannan sun zargi ECOWAS da mara wa manufofin Turawan Yamma baya wanda kuma hakan barazana ne ga ƙasashen biyu a cewar takardar sanarwar.
Wannan mataki na nuna yankewar alaƙar ƙasashen na shekaru 49 tun bayan kafa ƙungiyar a ranar 28 ga watan Mayun shekarar 1975.