Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar EFCC reshen Jihar Kano ta cafke ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya da ta yi suna da tabarujji da badala a jihar Kano sakamakon wulaƙanta takardar Naira..
Majiyar hukumar ta ce idan bincike ya kammala, za a gurfanar da ita a kotu domin fuskantar hukunci bisa laifin da ake zarginta da aikatawa.
- Farashin Kayan Abinci A Watan Azumi Ya Shammace Mu – ‘Yan kasuwa
- Mahaukaci Ya Yi Sandin Mutuwar Ango Da ‘Yar Uwar Amarya Mintuna Kafin Daurin Aure A Bauchi
Rahotanni sun nuna cewa an kama Murja kimanin makonni uku da suka gabata, amma ta tsere daga beli kafin sake kama ta a ranar Asabar ɗin.
Murja Kunya ta yi kaurin suna tun bayan fara amfani da kafafen sada zumunta a matsayin abin barkwanci, kafin daga bisani ta mayar da shi dandalin sana’a.
A tsawon lokaci, ta shahara musamman a TikTok, inda take amfani da sunan “Yagayagamen,” duk da cewa a bayan nan ta jawo ce-ce-ku-ce a kanta.
A bayan nan dai hukumar ta EFCC ta cafke wasu abokan sana’ar Murja ’yan TikTok irinsu Alamin G-Fresh da Ashir Idris kan makamancin wannan zargi na wulaƙanta takardun kuɗi.