Home » Falasdinawa 200 Sun Shaki Iskar ‘Yanci

Falasdinawa 200 Sun Shaki Iskar ‘Yanci

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP da na Reuters sun ce Isra’ila ta sako Falasɗinawa 200 daga cikin waɗanda take riƙe da su a kurkuku kamar yadda yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da ƙungiyar Hamas ta tanada.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Hamas ta saki rukuni na biyu na ’yan Isra’ilar da ta yi garkuwa da su.

A wata sanarwa da hukumomin gidan yari na Isra’ila suka fitar sun ce: “Bayan kammala dukkanin abubuwan da suka wajaba a gidajen yarin da kuma amincewar hukumomi an saki dukkanin ’yan ta’addan daga gidajen yari na Ofer da Ktziot,”

Sai dai sabanin Falasɗinawan da aka saki a makon da ya gabata waɗanda yawanci hukuncinsu na zaman gidan yari kaɗan ne, a wannan karon, 121 daga cikin fursunonin suna kan hukuncin rai da rai ne, wasu bisa laifin kisan kai fiye da sau daya da ya hada da kisan farar hula ’yan Isra’ila.

Shekarun Falasɗinawa fursunonin sun bambanta sosai, inda mafi ƙanƙanta da aka saki shi ne mai shekara 16, yayin da mai shekara 69 ya kasance mafi girma a cikinsu.

Ɗaya daga cikin fursunonin ya shafe shekara 39 a gidan kurkukun Isra’ila, bayan da aka kama shi da farko a 1986.

Waɗanda aka yanke wa hukuncin manyan laifuka mafiya tsanani ba sa cikin waɗanda aka saki yau.

Kusan 70 daga cikinsu za a fitar da su daga Isra’ila ne inda za a bi da su ta Masar zuwa ƙasashe makwabta da suka haɗa da Qatar da Turkiyya, kafin a kai su Falasɗinu.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?