Mutum daya na mutuwa a kowace sa’a a Ghana saboda cututtukan da za a iya magancewa da suka shafi ruwa da tsaftar muhalli.
Ramesh Bhusal, jagoran Shirin Ruwa da Tsaftar Muhalli na Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) a Ghana ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya sawa hannu inda yake cewa rashin tsaftar muhalli a kasar na haifar da babbar illa ga lafiyar al’umma.
Yayin da yake lura da cewa mutum daya ne ke mutuwa daga cututtukan da za a iya magancewa da suka shafi ruwa da tsaftar muhalli a kowace sa’a guda a kasar ta Ghana. Bhusal ya jaddada cewa bayar da fifiko ga aiyukan tsarin WASH a kasar zai taimaka wajen ceton rayuka.
Da yake nuni da cewa ruwa na da matukar muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki da walwalar kowace al’umma, Bhusal ya bayyana nadamarsa cewa wannan ‘yancin dan adam ba ya samuwa ga mutane da yawa.
Bhusal ya kuma yi nuni da cewa Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci mahukuntan Ghana da su gaggauta shawo kan lamarin ta hanyar kara zuba jari a fannin WASH domin samar da tsaftataccen ruwan sha ga jama’a.