Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce ta gudanar da wani samame na hadin guiwa da sauran jami’an tsaro a jihar Kogi a jiya inda tayi nasarar kama wasu gungun masu aikata laifuka su shida a Gegu Beki, da ke Lokoja kan hanyar Abuja.
Mai magana da yawun hukumar ta DSS, Dakta Peter Afunanya, ya sanar da haka a jiya.
Mutanen da aka kama sun haɗa da: kanal AU Suleiman (mai ritaya) da Barista MK Aminu da Kabir Abdullahi da Isah Umar da Kadir Echi da Adama Abdulkarim.
An kuma ƙwato makamai daga hannunsu da suka haɗa da bindiga mai ƙirar famfo guda ɗaya da ƙwanson alburusai 4, ƙwanson alburusan bindiga ƙirar AK47 guda daya da kudi Naira dubu N11,030.
Har ila yau, a ranar 25 ga Maris, 2023, jami’an sun kama wani matashi mai shekaru 20 da ake zargi da yin garkuwa da mutane mai suna Haruna Adamu, a kauyen Fotta da ke karamar hukumar Gombi ta jihar Adamawa.
Sannan ta kuma kama wani mai suna Aminu Ibrahim a ranar 23 ga Maris, 2023, wanda ake zargin ɗan bindiga ne a hanyar Kubwa Expressway, Abuja a lokacin da yake kan hanyarsa daga jihar Nasarawa domin kai alburusai 432 da aka boye a cikin galan din manja mai faɗin lita hudu da niyyar kai wa ‘yan bindiga da ke jihar Neja.
Hakazalika, hukumar ta kame Babangida Ibrahim, mai jigilar makamai zuwa ga ‘yan bindiga da ke jihar Zamfara a Jos ta Kudu ta jihar Filato.
Izuwa yanzu dai an gurfanar da dukkan waɗanda ake zargin gaban kotu domin girbar abin da suka shuka.