Wata gobara mai karfin gaske da iska sun afkawa dazukan kasar Isra’ila, inda aka ce al’amarin na cigaba da tsananta daga daren jiya Laraba zuwa wayewar yau Alhamis, abin da ya tilastawa Firaminista Benjamin Netanyahu sanar da dokar ta ɓaci tare da neman agajin ƙasashen duniya don murƙushe wutar wadda ta durfafi dazukan da ke gab da shiga birnin Ƙudus.
Wasu hotuna da bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna cewa an fara aikin kwashe mutanen da ke gab da yankin da wutar dajin ta kama.
- Gwamnan Bauchi Ya Kara Nada Wa Kansa Mataimaka168
- NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyin Naira Biliyan Daya A Kano Da Legas
Wutar dajin ta tilasta kulle babbar hanyar shiga Tel Aviv daga birnin Ƙudus ta yadda hayaƙi kawai ake hangowa daga cikin duwatsun da suka kewaye yankin.
Rahotanni na cewa mutane da dama sun bar motocinsu akan hanya don tsira da rayukansu sakamakon hayaƙin da ya turnuke yankin.

