• Home  
  • Gungun Yan Daba Sun Tare Motocin Yan Sanda Da Yan Jarida A Kano
- Babban Labari - Labarai

Gungun Yan Daba Sun Tare Motocin Yan Sanda Da Yan Jarida A Kano

Wasu gungun yan dabar siyasa sun tare motocin jami’an yan sanda da yan jarida a garin Janruwa dake karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano lokacin da suke kan aikinsu na duba yadda zaben cike gurbi yake gudana. Yan jaridar dai suna cikin masu daukar rahoto a hukumomin tsaron jihar , wadanda motarsu ta lalace, bayan […]

Wasu gungun yan dabar siyasa sun tare motocin jami’an yan sanda da yan jarida a garin Janruwa dake karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano lokacin da suke kan aikinsu na duba yadda zaben cike gurbi yake gudana.

Yan jaridar dai suna cikin masu daukar rahoto a hukumomin tsaron jihar , wadanda motarsu ta lalace, bayan sun bar garin Bagwai don zuwa karamar hukumar Ghari, tare da tawagar hukumomin tsaron wadanda aka barsu a baya.

Daga baya rundunar yan sandan jihar Kano, ta turo wasu motocin yan sanda don su tafi da yan jairdar da motarsu ta lalace, inda akan hanyarsu daidai garin Janruwa dake karamar hukumar Bagwai, gungun yan dabar siyasar suka tare motocin tare hana su wucewa.

jami’an yan sandan sun nuna kwarewar aiki wajen tsaratar da yn jaridar zuwa karamar hukumar Bichi, kafin su samu karin mataimaka don komawa wuraren da yan dabar ke shiga don tayar da hankali

Yan awannin kadan kenan kwamishinan yan sandan jihar CP Ibrahim Adamu Bakori ya bayyana cewa sun kama mutane 288 dauke da makamai wadanda ake zrginsu da yunkurin tayar da tarzoma a wuraren zabukan.

A  ranar asabar dinnan aka gudanar da zaben cike gurbin na yan majalissun jihar Kano, masu wakiltar kananan hukumomin Ghari/ Tsanyawa da kuma Bagwai da Shanono.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai