• Home  
  • Gwamna Abba Ya Roƙi A Sauya Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano. 
- Babban Labari - Labarai

Gwamna Abba Ya Roƙi A Sauya Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano. 

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nemi shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya gaggauta cire kwamishinan ‘yan sandan CP Ibrahim Adamu Bakori daga Jihar. Gwamnan Ya yi wannan kira ne a lokacin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar […]

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nemi shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya gaggauta cire kwamishinan ‘yan sandan CP Ibrahim Adamu Bakori daga Jihar.

Gwamnan Ya yi wannan kira ne a lokacin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata Kano.

Gwamnan ya yi Allah wadai da matakin Kwamishinan da ƴan sandan ya Dauka na janye jami’an tsaro a filin wasa na Sani Abacha inda ake gudanar da bikin ranar samun yancin kai.

Abba ya Kara da cewa a matsayin sa na shugaban Hukumomin Tsaron Jihar, Bai San dalilin janye Jami’an yan sandan cikin kankanin lokacin ba duk da muhimmancin da bikin yake da shi.

Kawo yanzu rundunar Yan Sandan Jihar Kano bata fitar da Wata sanarwa kan dalilin janye Jami’an da kuma rashin ganin Kwamishinan a wajen bikin cikar Nijeriyar Shekaru 65 da aka gudanar a Kano

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai