• Home  
  • Yan Bindiga Sun Halaka Mutane 3 Tare Da Sace Shanu 1,000 A Jihar Neja
- Babban Labari - Labarai

Yan Bindiga Sun Halaka Mutane 3 Tare Da Sace Shanu 1,000 A Jihar Neja

Wasu yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Magama , a jihar Naija inda suka halaka mutane 3 tare da sace shanu sama da dubu daya 1,000. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:00am na ranar Talata wadanda yan bindigar suka farwa kauyukan Ibeto, Salka da kuma Koso. Wani mazaunin yankin ya shaidawa Chennels tv , […]

Wasu yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Magama , a jihar Naija inda suka halaka mutane 3 tare da sace shanu sama da dubu daya 1,000. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:00am na ranar Talata wadanda yan bindigar suka farwa kauyukan Ibeto, Salka da kuma Koso. Wani mazaunin yankin ya shaidawa Chennels tv , cewa yan bindigar sun mamaye garin Kura da yammacin jiya talata. A cewarsa yawancin mazauna kauyen tsoro da firgi ya Sanya su buya a daji yayin da wasu kuma suka rufe kofofin gidajensu sakamakon farmakin da suka kai mu su.

 ‘’ yanzu yan bindigar sun nufi Dajin Magana da ya ratsa zuwa jihar Zamfara bayan sun gama ta’addancin su’’. Tuni wasu shaidun gani da ido suka yi kira ga gwamnatin jihar da ta tarayya su su kawo Karin jami’an tsaro a yankin.Mun yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Naija, SP Wasiu Abiodun, amma bai samu damar daga wayarsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.Wannan na zuwa ne kwana guda da yin garkuwa da tsohon shugaban hukumar Ilimin bai daya ta Jihar Neja (SUBEB), Alhaji Alhassan Bawa Niworo da wani lauya Barista Ahmad tare da wasu fasinjoji a ƙauyukan Felegi da Ibi a kan

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai