Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, ya amince da naɗin wasu ƙarin masu bashi shawara na musamman guda uku don ƙara inganta gudanar da aiki da haɓaka cigaba a jihar.
Wannan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da babban sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya sanya wa hannu.
Malam Bala Ibrahim ya ce an yi naɗin ne bisa cancanta da ƙwarewa da kuma sahihancin hali, domin tabbatar da jihar ta samu jagoranci daga mutane masu basira waɗanda ke da niyyar yin hidima ga al’umma.
Sabbin masu bada Shawarar da aka naɗa sun haɗa da Kabiru A. Sugungun,
a matsayin mai bada shawara a kan harkokin majalisar tarayya, da Ibrahim Ahmed Kwaimawa, a matsayin mai bada shawara na musamman kan harkokin masana’antu wato (Industrial Relations), sai kuma Ado Sani Birnin Kudu wanda zai bada shawara kan harkokin Ma’aikata wato (Civil Service Matters).
- Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Haifar Da Rudani A Garin Yelwa Musari
- Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas
Yayin da yake taya su murna, Sakataren Gwamnatin jihar ya bayyana tabbacin cewa sabbin jami’an za su bayar da gudunmawa mai ma’ana wajen cimma manufofi da tsare-tsaren gwamnati.
“Waɗannan nade-nade suna nuna jajircewarmu wajen samar da nagartaccen shugabanci tare da tabbatar da cewa jiharmu ta samu shugabanni masu sadaukarwa, ƙwarewa da gaskiya,” in ji shi.
Malam Bala Ibrahim ya yi kira ga jama’a da su ba da goyon baya ga sabbin masu bada shawarar na musamman yayin da suka fara gudanar da ayyukansu.
Inda ya ce naɗin na su ya fara ne nan take.

