Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya kafa kwamitin da zai kasafta gudunmawar kuɗi da sauran kayan amfani da jihar ta samu da suka tasar ma tsabar kuɗi Naira Miliyan Dubu huɗu.
Jihar Borno dai ta fuskanci mummunar ambaliya a kwanakin baya, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyi masu ɗimbin yawa. To sai dai mutane daga sassan ƙasar nan dama wajen ta sun bada tallafi na kuɗi da sauran kayan amfani, domin rage raɗaɗin ga mutanen da ambaliyar ta shafa.
Attajirai irinsu Alhaji Aliko Ɗangote da Alhaji Aminu Ɗan Tata da wasu masu riƙe da madafun iko duk sun bada tasu gudunmawar.
Gwamna zulum yace aikin kwamitin shine kasafta kuɗin gudunmwar domin ganin saƙon yaje gurin waɗanda lamarin ya shafa.