• Home  
  • Ba na nadamar cire tallafin mai —Tinubu
- Babban Labari

Ba na nadamar cire tallafin mai —Tinubu

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba ya da nadamar soke tallafin man fetur, yana mai jaddada cewa Najeriya ba za ta sake komawa tsarin ba. Ya kuma soki tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar ADC, kan alkawarinsa na dawo da tsarin tallafin. A cewar Tinubu, kafin gwamnatinsa […]

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba ya da nadamar soke tallafin man fetur, yana mai jaddada cewa Najeriya ba za ta sake komawa tsarin ba.

Ya kuma soki tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar ADC, kan alkawarinsa na dawo da tsarin tallafin.

A cewar Tinubu, kafin gwamnatinsa ta cire tallafin man fetur, Najeriya tana fuskantar barazanar durkushewar tattalin arziki.

Ya bayyana haka ne a ranar Litinin a wani taro da  kungiyar City Boy Movement tare da hadin gwiwar kungiyar Relax-Tinubu-Is-Fixing-Nigeria suka shirya domin nuna goyon baya ga sake tsayawarsa takara a shekarar 2027.

Tinubu ya kwatanta cire tallafin da labarin Annabi Musa (A.S) da Bani Isra’ila suka bar Masar, yana mai cewa Najeriya ba za ta koma baya ba.

“Lokacin da Annabi Musa ya fice daga Masar ya fuskanci kalubale, amma Tekun Bahar Maliya ya bude musu hanya. Bayan nan, ai ba za ka ce wa Annabi Musa ya koma Masar ba.

“A kullum muna tashi ne da sabbin tunani da dabaru domin ciyar da kasar nan gaba. Da goyon bayanku da kuzarin matasa, ba za mu koma Masar ba. Ba ni da wata nadama,” in ji shi.

‘Tattalin arziki na samun ci gaba’

Tinubu ya amince cewa shekaru ukun farko na gwamnatinsa sun kasance masu cike da kalubale, amma ya ce dole ne gwamnati ta dauki matakai masu tsauri domin ceto tattalin arzikin kasar.

Ya ce maimakon dora laifin matsalolin kasa kan gwamnatocin baya, ya zabi daukar nauyin warware matsalolin da ake fuskanta.

“Mun fahimci cewa kasa ba za ta iya aro kudi har abada tana sa ran samun ci gaba ba,” in ji shugaban.

Amma duk da haka, shugaban ya ce tattalin arzikin Najeirya yana ci gaba da ingantuwa sannu a hankali, yana mai bayyana kwarin gwiwarsa cewa kasar tana kan turbar da ta dace.

Ya bukaci magoya bayansa da su dauki zaben 2027 a matsayin fafutuka domin makomarsu, ba don amfanin dan takara kadai ba.

“Dole Najeriya ta yi nasara a wannan zabe kafin kowane dan takara. Ba ni kuke yi wa kamfe ba, makomarku ce kuke karewa. Wannan makoma ita ce Renewed Hope. Babu abin da zai mayar da mu baya,” in ji shi.

Tinubu ya jinjina wa matasa

Tinubu ya ce masu sukar manufofinsa sun yi hasashen cewa matasan Najeriya za su yi watsi da sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa, amma hakan bai faru ba.

“Sun yi kuskure. Kun zo nan kun nuna goyon baya,” in ji shi.

Gabanin zaben shugaban kasa da aka tsara gudanarwa a ranar 16 ga Janairu, 2027, shugaban ya bukaci matasa su yada sakonsa a cibiyoyin ilimi, kasuwanni da kauyuka.

Dangane da dokar lamunin karatu da ya sanya wa hannu a shekarar 2023, Tinubu ya ce ba ya da nadamarta, yana mai cewa sama da dalibai miliyan daya sun amfana da tallafin da Asusun Lamunin Karatun Najeriya (NELFUND) ke bayarw

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai