Gwamnan jihar Barno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ɗaukaka darajar kwalejin Mustapha Umar Elkanemi ta karatun Larabci dake Maiduguri zuwa matsayin babbar cibiya ta musamman ta koyar da ilimin larabci da ilimin addinin Musulunci.
Gwamnan ya ce, sun yi hakan ne domin yaƙi da irin fahimtar da ƴan ta’addar Boko Haram suka yi wa Karatun Addinin Musulunci wanda ya gurguntar da al’amuran cigaba a faɗin jihar da ma ƙasar nan baki ɗaya.
GA CIGABAN RAHOTON: