Gwamnan ya dauki matakin ne da nufin kare irin wadannan masu sana’a, daga kisan da ‘yan Boko Haram ke yi a wajen garuruwan kananan hukumomin jihar.
Ba a san adadin matasan da aka kashe sakammakon irin wannan sana’a a hanyarsu ta tafiye-tafiye zuwa garuruwa ba.
Da yake sanar da matakin, Gwamna Zullum, ya ce,” A cikin shekaru biyar da suka wuce, an kashe mutane da dama a sakamakon yawan jari bola da suke abin da ya janyo gwamnatin jihar ta fara bincike a kai ke nan.”
Zullum, ya ce yawancin masu irin wannan sana’a kuma na lalata kayayyakin gwamnati da ma na kamfanoni masu zaman kansu a don haka ba za a amince da irin wadannan mutane ba.
Gwamnatin jihar ta ce za ta yi aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro don tabbatar da an kama duk wanda ya yi kunnen kashi ko ya karya doka.