Home » Hukumomi a Hadeja sun haramta barace-baracen yara mata a yankin

Hukumomi a Hadeja sun haramta barace-baracen yara mata a yankin

by Anas Dansalma
0 comment
Magnificent Century Episode 38

Hukumomi a yankin Hadejia da ke jihar Jigawa sun dauki matakin hana barace-baracen yara mata matasa da ma sauran nau’o’in bara, bayan da aka samu wasu mata mabarata da juna biyu tare da mayar da su garuruwan su na asali.

Bayanai na nuna cewa mabaratan maza da mata suna kwarara ne cikin garin Hadejia daga ciki da wajen jihar Jigawa, don yin bara inda suke bi tashoshin mota da kasuwanni.

A baya-baya matsalar ta yi kamari inda mazauna yankin suka ce al’amarin ya kai ga ana cin zarafin wasu daga cikinsu.

Game da wannan matsala dai karamar hukumar Hadejia ta samar da wani kwamiti wanda ya bincika batun sannan ya bayar da shawararin abin da ya kamata a yi.

Akasarin matan da aka kama din ba su da takamaiman wurin kwana.

Mahukunta a Hadejan sun ce yaran da suke gararamba ‘yan asalin karamar hukumar Hadejan musamman marasa galihu, za a yi musu tsari don samar musu da matsuguni tare da sanya su a makaranta.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?