Gwamnan Jihar Katsina Dokta Umar Dikko Radda ya jinjina wa jami’an tsaron Nijeriya kan nasarar da suka samu wurin kashe ‘yan ta’adda 80 a jihar.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Katsina Dakta Nasir Muazu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar. Ya ce sojojin sama na Operation Fansan Yamma da sojojin Biriged na 17, da ‘yan sanda da jami’an tsaron DSS da kuma jam’ian sa-kai na bijilante ne suka gudanar da wannan aikin a ranar 4 ga watan Janairun da muke ciki.
Sanarwar ta bayyana cewa jami’an tsaron sun kai samame sansanonin ‘yan bindigar da ke Kadoji da Matso-Matso da Bagga da Dogon Marke da Takatsaba da ke yankin Jibia.
Hakazalika Sojojin Operation Fansar Yamma a Jihar Zamfara a ranar 4 ga Janairu sun yi arangama da ‘yan ta’adda a ƙauyen Bamamu a Ƙaramar Hukumar Tsafe da ke Zamfara.
Sai dai nasarar da jami’an tsaron suka samu na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan bindiga suka kashe shugaban riƙo na ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah a Katsina, Alhaji Surajo Amadu Rufa’i.
‘Yan bindigar sun kashe shi ne a gidansa da ke ƙauyen Marina a Ƙaramar Hukumar Kusada.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da lamarin, inda ya ce bayan sun kashe Rufa’i, sun yi garkuwa da matarsa da ‘yarsa.