Babu shakka Karas na da matukar amfani ga jikin dan adam musamman ma idanu. karas yana kunshe da sinadirai masu tarin yawa daga cikin su akwai sinadarin B-carotene da ke matukar taimaka ma lafiyar idanu.
Binciken masana ingantaccen abinci sun bayyana cewa bayan karin dandano da karas yake karawa abinci yana kuma dauke da sinadarai masu yawa masu inganta lafiya.
Kamar yadda binciken masana kiwon lafiya ya tabbatar, yawan cin Karas na matukar taimakawa ta fuskar inganta lafiyar Dan Adam daga bangarori daban-daban.
Karas Yana dauke da sukari mai dimbin yawa Ya kamata mutane da ke da cutar sukari da aka fi sani da diabetes su yi taka tsan tsan game da cin karas domin yana dauke da sukari mai yawa.
Jikin dan adam na sauya sukarin da ke cikin karas zuwa glucose wanda shi kuma ke kara adadin sukarin da ke jinin dan adam cikin gaggawa. Idan ya zama dole mai ciwon diabtes zai ci karas, ya fi dace wa ya dan dafa karas din kuma ya ci kadan.
A sakamakon sunadarai da karas ya kunsa, ga cututtuka da yake taimakawa gurin warkarwa.
- Taimakawa wurin kiyaye kamuwa da ciwon daji (kansa) Karas na dauke da sinadarai masu yawa da masana ke kira ‘Phytochemicals’ da ke yaki da cutan daji. Wadannan sinadaren na karfafa garkuwar jiki. Masana sun kuma gano karas na iya maganin Leukemia da kare yiwuwar kamuwa da ciwon daji na baki.
- Karas na dauke da sinadarin vitamin A wanda yake Inganta Lafiyar Ido yana taimakawa idanu su rika gani tangaran kuma karas na dauke da Vitamin A masu yawa.
- Karas na dauke da sinadarai masu yawa da ake kira ‘carotenoids’. Binciken ya nuna cewa ‘ya’yan itatuwa da ganyeyyaki suna dauke da sinadarai na ke inganta lafiyar mutum ya kuma haskaka fatarsa Sai dai cin karas din fiye da kima yana iya haifar da matsala mai suna ‘carotenosis’ da ke saka fatar mutum tayi haske da yawa.
- Bugun Zuciya Wani sabon bincike da masana kimiyya suka gudanar ya nuna cewa ruwan da aka tatsa daga karas na rage hawan jini da kashe 5 cikin 100. Sinadaren da ke cikin karas da suka hada da fibre, potassium, nitrates da Vitamin C ne ke taimkawa wurin wannan.
- Taimakawa masu ciwon suga Cin abinci mai inganta lafiya yana taimakawa wurin rage kiba da kuma hana kamuwa da ciwon suga nau’i na biyu. Bincike ya nuna cewa Vitamin A na kare afkuwa da kamuwa da ciwon suga kuma tunda karas na kunshe da sinadarin sosai yana iya taimakawa.
- Karfin kashi Vitamin A yana taka muhimmiyar rawa wurin gyara kashin dan adam. Beta-carotene da karas ke dauke da shi yana kare kwayoyin hallita daga cututuka kuma yana taimakawa inganta lafiyar kashi.
- Cututtukan baki da hakori Danyen karas yana taimakawa wurin kawar da kwayoyin cuta daga hakora kuma ya washe numfashin mutum. Fibre da karas ke dauke da shi yana kara adadin yawu a bakin mutum da ka iya taimakawa ya rage adadin citric acid a malic acid da ke bakin dan adam.