Daga Mujahid Wada Musa
Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta yi bikin kara wa jami’an ta 272 girma, a matakai daban-daban kamar yadda hukumar kula da aiyukan yan sanda ta kasa PSC ta amince.
An gudanar da bikin karin girman a wajen shakatawar manyan jami’an yan Sanda dake unguwar Bompai a ranar Litinin.
Kwamishinan yan sandan jihar Kano CP Salman Dogo Garba, ya taya wadanda suka samu karin girman, Inda yaja hankalin su kan ci gaba da jajircewa kan aikinsu.
- Gwamnan Jihar Katsina Ya Jinjina Wa Jami’an Tsaro
- An Dauki Matakin Ba Sani Ba Sabo Kan Komawa Makarantu A Kano
Cikin wadanda likafar ta su ta daga sun hada da, mataimakan kwamishinan yan sanda 4, sai mutane 50 daga matakin SP zuwa CSP sai mutane 32 daga DSP matakin zuwa SP da kuma mutane 286 daga matakin ASP zuwa DSP.
Rundunar ta ce wannan rana ce ta farin ciki agare su, da wadanda suka samu karin girman da kuma iyalansu.